AURATAYYA
◽Wannan manhajar ta ƙunshi shiri da zai tattauna akan abunda ya shafi ma'aurata, da koyar da sanin haƙƙoƙin aure tsakanin ma'aurata yanda kowane ma'auraci zai saukewa ɗaya abokin zaman nasa haƙƙin sa.
◽ Aure wata yarjejeniya ce tsakanin namiji da mace wanda kowane yake neman samun biyan buƙata da jindaɗi da ɗayan, tare da gina rayuwar iyali ta gari wanda ke kaiwa ga samar da tabbatacciyar al'umma.
Domin samun rayuwar aure mafificiya akwai buƙatar ɗaukar matakai guda uku, wanda zakuji su a cikin wannan shiri, wannan shiri ya ƙunshi duk wasu bayanai da ya kamata ma'aurata su sani domin inganta rayuwar auren su, sannan waɗanda suke shirin zama ma'aurata suma akwai abubuwan da ya kamata su sani kafin suyi auren, duka waɗannan abubuwa anyi bayanin su a cikin wannan manhajar.
ABUBUWAN DA MANHAJAR TA ƘUNSA: 🔹Bayanin abubuwan da suka kamata ga waɗanda suke son yin aure su san su. 🔹Bayanin abubuwan da ma'aurata zasu kiyaye domin inganta rayuwar auren su. 🔹Bayanin yanda za'a warware matsaloli a zamantakewar aure ga masu fuskantar matsaloli a auren su.Wannan manhajar zata taimaka sosai da kawo gyara a zamantakewar auratayya in sha Allah.